What is HIBAF?

The Hausa International Book and Arts Festival (HIBAF) will be curated by Open Arts as a crisscross festival of arts and language. It is the aim of this festival to open up discussions about Hausa as a language through literature, history, music and arts to be displayed to a new and exciting young audience.


The festival aims to showcase the best of contemporary African literature, poetry, music, art, film, and theatre in Hausa to a target audience of thousands of youths across West Africa. This is an important period in West Africa at crossroads of extremism to consider arts in Hausa as focal points to address our problems. We hope to combine the tools of arts and literature through new digital collaborations and conversations to seek fresh perspectives about the role and meaning of culture in a time of crisis.

BIKIN BAJE KOLIN LITTATTAFAI DA FASAHOHIN HAUSAWA NA KASA DA KASA, 2021

 

Bikin Baje Kolin Littattafai da Fasahohin Hausawa Na Kasa Da Kasa Na Shekarar 2021 da OPEN ARTS za ta gabatar zai kasance biki ne na tattauna rayuwar Hausawa da harshe da al’adu da adabin Hausa, domin karuwar matasan Hausawa da sauran al’umma baki daya.

 

Babban burin wannan biki shi ne ya fasalta da gabatar da kyawawan dabi’u da adabin al’ummar Nahiyar Afirka ta amfani da fasahoihin waka da kade-kade da fina-finai da karanta littattafai. Wannan biki ya zo daidai a lokacin da ake bukatar wayar da kan al’umma ta amfani da adabi da al’adun Hausawa dangane da matsalolin da ke addabar al’ummar Yammacin Afirka. Wannan biki zai kasance na hadakar al’adu na gargajiya da fasahohin zamani domin samar da mafita, musamman bisa la’akari da halayen tashin-tashina da ake ciki yanzu.

 

Taken Bikin Baje Kolin Littattafai Da Fasahohin Hausawa Na Kasa Da Kasa Na Shekarar 2021 shi ne  ‘Sarari’. Wannan bikin a karon farko zai dubi abubawa da ke tattare da sarari da abin da ke tsakani; sararin asalin al’umma da harsunansu, sararin kasancewa al’umma a tsawon tarihi; sararin samar da labarai da ginuwar mutuntakar al’umma; yadda za mu iya tu’ammali da kowane sarari na jaddada asali cikin rayuwar ayyanannen adabi. A cikin sararin wannan bikin baje koli na bana, za mu dubi asalin samuwar ayyukan adabin Hausawa, inda za a tattauna alakar da ke tsakanin jinsin al’umma da al’adu da siyasa. Shi sarari kamar yadda aka sani yana tattare da al’adu mabambanta, kamar kwalliyar tufafi da kayan ado da kuma adabi. Babban kudurin wannan bikin baje koli shi ne ta’allaka sararin ayyanawa da na zahiri ta amfani da harshe mai burgewa da armashi ta yadda za a samar da sararin da zai ba kowa damar baje kolin tunani da kasafta rayuwar al’umma bisa faifan yarda da aminci da dacewa.

A karon farko wannan bikin baje kolin littattafai da fasahohin Hausawa zai zama sarari na warkarwa ga makaranta da marubuta; sarari ne da zai tsokano matsaloli ya magance su; sarari ne da zai kasance cunkushe da labarai da wakoki da raye-raye da kade-kaden  Hausawa da za a gabatar ta hanyar Shoshiyal Midiya da kuma rubdugu a sararin subhana daga ranar 21 ga Oktoba zuwa 23 ga Okotoba 2021 a garin Kaduna, Nijeriya.